Ya ku mutane, an ba da misali, to sai ku saurare shi. Lalle waxanda kuke bauta wa ba Allah ba,...

Ya ku mutane, an ba da misali, to sai ku saurare shi. Lalle waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba za su tava iya halittar quda ba, ko da sun taru domin (halitta) shi; idan kuma da qudan zai cire musu (su gumakan) wani abu, to ba za su iya qwato shi ba daga wurinsa. Wanda yake nema da wanda ake nema (duka) sun yi rauni!