Allah kuma Ya ba da misali da bawan da aka mallaka,...

Allah kuma Ya ba da misali da bawan da aka mallaka, ba shi da iko a kan komai, da kuma wanda Muka bai wa arziki nagari daga gare Mu, to shi kuma yana ciyarwa daga shi (arzikin) a voye da kuma sarari; yanzu za su yi daidai? (Ai ba za su yi daidai ba). To godiya ta tabbata ga Allah. A’a, yawancinsu dai ba su san (haka) ba ne